Labaran Kano
Kano: mai amfani da kafafen sada zumunta ya zargi rundunar ‘yan sandan Kano da cin zarafinsa
Wani kwararre a fannin kafafen sada zumunta jihar Kano, Bashir Bashir Galadanci ya kai karar kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Kano bisa zargin cin zarafinsa tare da take masa ‘yanci a matsayinsa na dan-Adam.
Jaridar Kano Focus ta ruwaito cewa, Bashir Galadanchi ya zargi kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, da tsare shi ba bisa ka’ida ba, tare da azabtar da shi yayin bincike da kuma tursasa shi amsa laifin da bai aikata ba.
Idan za’a iya tunawa dai an kama matashin ne a ranar 11 ga watan Satumban da ya gabata bisa zarginsa da bayyana wasu bayanai da suka shafi rundunar ‘yan sandan ba tare da amincewarsu ba.
A wani bidiyo da ya dinga zagawa a kafafen sada zumunta na Internet, an nuna Bashir Galadanchi yana baiwa rundunar ‘yan sandan hakuri bisa laifin da ya aikata, tare da cewa tsohon kakakin rundunar ne ya dauki nauyinsa wajen kushe rundunar ‘yan sandan Kano.
A wata wasika da lauyan Bashir Galadanchi Abba Hikima ya aikawa kwamashinan ‘yan sandan jihar kano, ya bayyana cewa bidiyon da ya zaga gari na cewar Bashir din na bada hakuri ga laifin da ya aikata ya yi shi ne cikin matsi da takura.
Wasikar mai dauke da kwanan wata 25 ga wannan wata na Nuwamba ta bayyana cewar, an tsare shi ne na tsawon kwanaki biyar ba tare da wata takarda daga kotu ba, tare kuma da azabtar da shi, da jami’an tsaro na SARS suka yi bisa umarnin kakakin rundunar.
Haka kuma ya zargi DSP Abdullahi Haruna Kiyawa da cewar ya tursasa shi ya bata sunansa da kansa da kuma hana belinsa, bayan dukan da ya sha har sai da jini ya fito ta kunnensa kamar yadda lauyansa ya bayyana.
Sun dai bukaci rundunar ‘yan sanda jihar Kano da ta bincikI al’amarin tare da daukar matakin da ya dace.