Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Ra'ayoyi

Kano na buƙatar manya masu kunya, mutunci, ilimi da sanin yakamata – Ra’ayin Mubarak Lawan

Published

on

Daga Mubarak Ibrahim Lawan
Da yawan mutane sun raina manya da shugabanni a wannan zamanin sakamakon yanda su manyan suka wulaƙantar da kawunansu. Tun daga gida, iyaye sun daina keɓancewa don tattauna saɓaninsu a cikin gida.
A gaban yara su ke musayar yawu. A masallatai an daina mutunta manya da waɗanda ke da kamala ta sutura da ilimi. Ƴan shekaru kaɗan baya, in ka shiga Masallaci ba hula, to ba ka isa tsayawa a sahun gaba ba.
Saɓanin yau, a loton da ya gabata, gurin hirar manya daban da na yara.
Don haka, yaro ba zai taɓa ganin saɓanin yayunsa ba, ballantana na iyayensa. Zancen da duk ya yi nauyi ma ba a faɗarsa a gaban yara. Kodayake, kafafen sadarwa sun taka rawa mai yawa wajen gabato da nesa kusa, da kuma fitar da sirri fili. Duk da haka, da a ce iyaye sun cigaba da alkinta kyawawan halayen nan da a ka gada, to da ba a lalace ba haka.
Waɗancan tadojin ne suka sa a ka samu shugabanni masu kunya, ƙima, daraja da mutunci, musamman a yankunanmu na Arewa.
Koda wani zai ce ai suma shugabannin irin na yanzu ne, to na da ɗin sun yi nasarar ɓoye ƙazantarsu daga idon al’umma sakamakon wancan gadon kyakkyawa.
Wannan kuma ya sa ba a raina su ba; a ka ƙimanta su har zuwa mutuwarsu, wasunsu ma a ke yabonsu har yau.
Daga halin ɓera, danniya, murɗiya da babakeren da shugabanni ke nunawa a yau, zuwa alƙawuran ƙarya da suke ɗauka, hakan ya sa al’umma su ka dawo daga rakiyarsu.
Ko da dai wasu shugabannin siyasar baya sun yi Ta-maguzawa ga juna, sun sa an sassari juna, amma su kam sun nuna kishin jama’a, sun mutunta jama’a, kuma sun yi ma jama’a ayyukan da har yanzu a na mora.
Wannan ya banbanta su da na yau, waɗanda ba kishin ƙasa tare da su, ba na al’ummarsu, kuma ga mummunan hali.
Daga saɓanin Tsohon Sarki, Sanusi II, da gwamnatin Kano, yayyaga masarauta, ƙwatar zaɓe, cefanar da filayen gari; tsallake-tsallake na wasu ƴan siyasa tsakanin jam’iyyu don buƙatar kansu ba na al’umma ba, zuwa dambe tsakanin manyan gari a bainar jama’a, duka mutuncin shugabannin ya tsiyaye.
Tabbas muna buƙatar manya masu kunya, mutunci, ilimi da sanin yakamata. Muna buƙatar gayawa kanmu gaskiya don gyaran gobenmu aƙalla! Allah ya ba mu ikon gyarawa!
Mubarak Ibrahim Lawan
Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!