Labarai
Kano na ci gaba da samun nasara a wasannin neman cancanta na matasa
Tawagar jihar Kano data kunshi ‘yan wasan Kwallon hannu da ta Kwando sai zari ruga da Volleyball da Kwallon kafa a wasannin matasa na fitar da gwanaye zuwa wasan matasa na kasa ‘yan kasa da shekaru 15, na cigaba da samun galaba a wasanni daban -daban.
Gasar wacce ake gudanar da ita , ta shiyyar jihohin Arewa maso Yamma (Northwest Zonal Elimination)da jihohi Bakwai ke fafatawa a Kebbi kawo yanzu jihar Kano ta samu tikitin shiga zuwa babbar gasar ta kasa a wasanni Uku na Kwallon Kwando da Zari Ruga sai Volleyball.
A wasanni da aka fafata , Kano ta samu galaba akan tawagar jihar Kaduna a wasan zari Ruga ta mata da maki 21 da 7, ya yinda a bangaren maza , kungiyar ta samu tikitin kai tsaye sakamakon rashin abokiyar karawa daga sauran jihohi.
Daga kwallon kwando tawagar maza ta kare a mataki na biyu, bayan doke Katsina da ci 9 da 5, inda jihar Kaduna ta yi na daya, da hakan ya baiwa jihohin damar wakiltar yankin a gasar ta kasa mai zuwa a birnin Ilorin na jihar Kwara.
Haka ‘yan wasan Volleyball na maza ta jihar , sun kai banten su bayan samun nasara akan jihar Kebbi da ci 2-1, da kuma Sokoto da 26-24 , a wasan da aka kai ruwa rana tsakanin kungiyoyin.
A bangare daya kuma ana dakon wasan kwallon kafa tsakanin Kano da Kaduna a wasan dab da karshe wato ‘semi final ‘Asabar 04 ga Satumba 2021, da shima ake kyautata zato jihar zata samu galaba zuwa mataki na gaba da hakan zai bata tikitin zuwa birnin na Ilorin
You must be logged in to post a comment Login