Labaran Kano
Kano na da daliban sakandire fiye da dubu dari bakwai (700,000)
Jahar Kano na da daliban makarantun sakandare da suka haura dubu dari bakwai.
Shugaban hukumar kula da manyan makarantun sakandire na jahar Kano Dr Bello Shehu ne ya bayyana hakan ,lokacin da yake tattaunawa da filin Barka da Hantsi na nan gidan Rediyan Freedom.
Dr Bello yace duk da wadannan tarin dalibai na makarantun sakandire da jahar Kano take da shi,maaikatan da hukumar kula da makarantun sakandiren ta jahar Kano ke dasu dubu goma sha bakwai ne kawai.
Wadannan maaikata sun hada da kowa da kowa da ya kama da malaman gabadaya, da kuma sauran maaikata na bangaren mulki da masu gadi da masu shara da masinjoji.
Dr Bello ya kara da cewa tun zuwan sa hukumar a ranar 4 ga watan Yuni na shekarar bana, sun fito da tsare tsare da zai habaka karatun sakandire a jahar Kano.
Yace malamai da dama da suka samu damar zuwa karo karatu kuma suke nokewa ,ya da wo dasu domin cigaba da gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.