Wasanni
Kano Pillars ta yi rashin nasara a hannun Wikki Tourist

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ta yi rashin nasara a hannun abokiyar ta, ta Wikki Tourist a wasan mako na 22 a gasar firimiyar kasa ta NPFL wasan da ya gudana a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa dake jihar Bauchi.
Rashin nasarar ta Pillars na zuwa ne bayan da Abia Warriors, ta doke ta har gida a wasan mako na 21 a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata.
Wannan rashin nasara ta kara janyo wa kungiyar koma baya a kokarin da ta ke yi na neman kare matsayin ta a gasar mai daraja ta daya a Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login