Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

NPFL: Kano Pillars tayi rashin nasara har gida a hannun Rivers United

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars tayi rashin nasara har gida a hannun Rivers United da ci daya mai ban haushi.

Filin wasa na Ahmadu Bello da ke Zaria dai shi ne ya karbi bakuncin wasan da ya gudana a ranar Laraba 02 ga Maris din 2022.

Kuma fafatawar itace mako na 16 a gasar ta Firimiya mai taken NPFL da kungiyoyi 20 ke fafatawa.

Tsohon dan wasan gaban kungiyar ta Kano Pillars Nyima Nwagua ne ya zura kwallon a minti na 70 da ta bawa Rivers United nasara a wasan.

Pillars dai na ci gaba da samun koma baya a gasar ta bana, musamman yadda take gaza samun nasara a wasannin da ta ke bugawa.

A sauran wasannin mako na 16 da aka fafata a ranar Laraba sun hada da

Niger Tornadoes 1-1 MFM

Sunshine Stars 3-1 Heartland

Enyimba 2-1 Remo Stars

Katsina United 4-1 Dakkada FC

Lobi Stars 0-2 Plateau United

Akwa United 2-0 Wikki Tourist

Gombe United 1-0 Abia Warriors

Kano Pillars 0-1 Rivers United

Nasarawa United 1-1 Kwara United.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!