Labaran Wasanni
Kano ta lashe Zinare da Azurfa da Tagulla bayan buɗe gasar Para Games
Biyo bayan fara gasar wasanni ta masu buƙata ta musamman na ƙasa karo na farko , jihar Kano a Litinin 11 ga Afrilu, ta fara gasar da ƙafar dama bayan da ta lashe lambobin Zinare Biyu da Azurfa ɗaya.
‘Yan wasan motsa jiki na Para Athlete da suka haɗa da Lawan Bashir sai Safiyanu Abdullahi Ibrahim da Shu’aibu Abdullahi Ismail, sun lashe Lambobin Zinare da Azurfa da Tagulla gasar.
A wasan ƙwallon ƙafa ta Para Soccer , Kano ta tashi wasa 1-1, da jihar Plateau , bayan da ɗan wasa Abdullahi Muhammad (Ortega ), ya ramawa Kano ƙwallon da aka saka mata , a zagaye na biyu na wasan da aka kai ruwa rana tsakanin jihohin biyu.
Haka zalika ɗan wasan Kano na wasan ƙwallon Tebur na Tennis wato Para Table Tennis, Gbenga Osinawo , ya samu galaba akan ɗan wasan Kwara Mustapha Alanamo, daci 11 da 4 da 11 da 5 sai 11 3, da ya bada jumullar 3-0.
A bangare ɗaya ‘yan wasan na Kano, na cigaba da fafata wasanni daban -daban, a gasar da suka haɗa da wasan Kurme (Swimming), sai ƙwallon ƙafa ta (Deaf Soccer),da sauran wasannin motsa jiki na (Athletics ), a gasar da aka shiga rana ta biyu, bayan ƙaddamar da ita , a babban filin wasa na Moshood Abiola, dake birnin tarayya Abuja , da anan ake buga wasannin.
You must be logged in to post a comment Login