Labarai
Kano: Yan Bindiga sun hallaka wata mata tare da sace mutane 3 a Tsanyawa

‘Yan Bindiga sun hallaka wata mata tare da yin garkuwa da mutane uku a kauyen ‘Yan kamaye dake karamar hukumar Tsanyawa a daren jiya Asabar.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun shiga garin ne da misalin karfe 11 na daren jiya Asabar lokacin da al’ummar garin kowa ya kwanta Bacci.
Rahotanni sun tabbatarwa da jaridar cewa ‘yan ta’addan sun ajiye Baburan da suka taho da su a bayan gari, inda suka shiga da kafa don gudun hayaniya.
A cewar majiyar, maharan sun harbi wata Dattijuwa dake kokarin dakatar da su bayan da ta rika rokon su kan kada su tafi da danta.
You must be logged in to post a comment Login