Labarai
Kano: Yawan ƙuri’un zaɓen ƙananan hukumomi sun zarce na zaɓen Gwamnan 2019
Yawan ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen ƙananan hukumomin Kano sun haura ƙuri’un da jam’iyyar APC da PDP suka samu a zaɓen gwamna na shekarar 2019.
A sakamakon ƙarshe na zaɓen gwamna a shekarar 2019 ya nuna cewar, gwamnan Abdullahi Ganduje na APC ya samu ƙuri’u 1,033,695.
Yayin da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar PDP ya samu ƙuri’u 1,024,713.
Jimilla baki ɗaya jam’iyyun biyu sun samu ƙuri’u 2,058,408.
Karin labarai:
Babu fashi makarantu su koma bakin aiki-Ganduje
APC ce za ta lashe zaɓen ƙananan hukumomi baki ɗaya – Ganduje
A sakamakon ƙarshe na zaɓen ƙananan hukumomi da shugaban hukumar Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya fitar.
Ya ce, an kaɗa ƙuri’u 2,350,577 a zaɓen na ranar Asabar.
Ku kalli bidiyon sanarwar Farfesa Sheka.
Hakan na nufin ƙuri’un da aka kaɗa sun zarta waɗanda Gwamna Ganduje da Abba Kabir na PDP suka samu baki ɗayansu.
Gabanin zaɓen dai masana siyasa irin su Farfesa Kamilu Sani Fagge na jami’ar Bayero sun yi hasashen cewa za a samu ƙarancin jama’a a zaɓen.
You must be logged in to post a comment Login