Labarai
Kano: Za mu dinga bibiyar kananan hukumomi kan sarrafa kudaden su
Majalisar dokokin jihar Kano ta ce za ta rika bibiyar yadda kananan hukumomin jihar ke sarrafa kudadensu domin tabbatar da cewa, ayyukan da suke yi ye dace da bukatun al’ummar su.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Isyaku Ali Danja ne ya bayyana haka bayan da ya jagoranc kwamitin majalisar dokokin jhar ta Kano domin
tantance kasafin kudin wasu daga cikin kananan hukumomin jihar ta Kano.
Ya ce wajbi ne majalisar ta rika sa ido kan yadda ake sarrafa kudaden wanda hakan zai tamaka gaya wajen kyautata rayuwar alummar karkara da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar.
Da ya ke zantawa da manema labarai bayan kare kunshin kasafin kudin karamar hukumar sa, shugaban karamar hukumar Rano, Alhaj Ya’u Abdullahi Gidan Dangi, cewa ya yi jin dadi da walwalar al’ummar yankin na daga cikin ayyukan da za su sanya a gaba a shekara mai zuwa.
Majalisar dokoki ta Kano ta amince da dokar kafa masarautu 4
Kai tsaye: An dage cigaba da zaman majalisar Kano
Kano: Majalisar dokoki zata gudanar da taron jin ra’ayin jama’a ranar 5 ga watan gobe
A nasa bangaren shugaban karamar hukumar Kumbotso Alhaji Kabiru Ado Fanshekara, ya ce, gina tituna shine bangaren da za su fi bai wa fifiko a badi.
Wakilin mu na majalisar dokokin jihar Kano Abdullahi Isah ya ruwaito shugaban karamar hukumar Munjibir, Nasiru Garba Kunya na cewa, karamar
hukumar za ta yi hadin gwiwa da gwamnatin jiha wajen ciyar da yankin gaba