Labarai
Kantin Jifatu ya fada komar dakarun tsaftar muhalli
Ma’aikatar muhalli ta jihar Kano ta rufe kantin Jifatu da ke titin zariya road tare da cin tarar sa naira dubu dari 2.
Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bada umarnin rufe kantin yayin duban tsaftar muhalli na yau asabar.
Matakin dai ya biyo bayan ci gaba da kasuwanci da kantin yayi daidai lokacin da ake tsaftar muhalli.
Tuni mai shari Auwal Sulaiman da ke jagorantar kotun tafi da gidanka kan tsaftar muhalli ya bukaci a rufe kantin kuma su biya tarar.
You must be logged in to post a comment Login