Kasuwanci
Karancin samun bashi daga gwamnati na haifar wa masu kananan sana’o’i nakasu- Minista
Gwamnatin tarayya ta ce, karancin samun tallafin bashi da masu kananan sana’o’i ke fuskanta daga gwamnati ya na haifar da tsaiko ga ci gaban tattalin arzikin Nijeriya.
Ministan kasuwanci da masana’antu Otunba Adeniyi Adebayo ne ya bayyana hakan a wani taron kara wa juna sani kan muhimmancin bada tallafin bashi ga masu kananan sana’o’i.
Adebayo ya kuma nuna damuwarsa kan irin kalubalen da masu gudanar da irin wadannan sana’o’i ke fuskanta idan suna son karbar bashi don inganta sana’arsu, da kuma yadda ake sanya kudin ruwa a cikin lamarin.
Ministan ya kara da cewa tun a watan Maris din shekarar da ta gaba ta gwamnatin tarayya ta amince da kafa hukumar da za ta kula da al’amuran da suka shafi karbar bashin da masu sana’o’i ke yi don inganta sana’o’in su.
You must be logged in to post a comment Login