Labarai
Karancin shan Ruwa na sabbaba kamuwa da ciwon Koda- Dr. Kamal Ahmad
Wani masani a fannin kiwon lafiya da ke aiki a Asibitin Abubakar Imam a jihar Kano Dakta Kamal Ahmad Habib ya bayyana cewa karancin shan ruwa na iya jawo hadarin kamuwa da ciwon Koda.
Dakta Kamal Ahmad Habib ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da Freedom Radio.
Ya ce, karancin shan ruwan na haifar da bushewa da dunkulewar wasu sinadari ta yadda suke komawa kamar dutse a magudanar fitsari da a harshen Turanci ake jira da Kidney Stone.
Ya kara da cewa su ne idan sun taru suke toshe kafoffin gudanarsa daga koda zuwa mafitsara.
Haka kuma, ya kara da cewa a kwai bukatar maza su sha ruwa a kalla Lita 3.7 kwatankwacin Kofi goma sha uku da rabi a ko wane wuni, yayin da ake bukatar Lita 2.7 kwatankwacin Kofi tara da rabi ga mata.
Jami’in, ya kuma ja hankalin mutane da su yawaita shan ruwa domin guje wa kamuwa da ciwon Koda.
You must be logged in to post a comment Login