Labarai
Karin wutar lantarki an yi shi bisa tsari kuma ba zai shafi talaka ba – KEDCO
Kamfanin rarraba wutar lantarki a jihohin Kano da Jigawa da Katsina KEDCO ya ce, karin farashin wutar lantarki an yi shi cikin tsari, kuma baya nufin matsantawa ga al’ummar kasar nan.
Shugaban sashin dabarun kasuwanci da tsare tsare na kamfanin KEDCO Ahmad Sunusi ne ya bayyana hakan a yau, jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan tashar freedom Rediyo da ya mayar da hankali kan batun karin farashin wutar lantarki.
Ya ce, tsarin da ya janyo karin farashin wutar lantarki zai tabbatar da samar da wadataccen hasken lantarki na tsawon awanni fiye da wanda aka saba sha a lokacin baya wanda kuma ba zai shafi mai karamin karfi ba.
Ya kuma ce tsarin shan wutar an raba shi kashi biyar sakamakon baiwa kowanne mataki na mutane damar shan wutar da suke bukata.
Ahmad Sunusi ya kuma ce, tsarin sai mutane sun bada gudunmawa na biyan kudi akan lokaci sannan za a samu damar samar da dawwamammiyar wuta a jihohin na su.
You must be logged in to post a comment Login