Labarai
KAROTA ta kai sumame Gandun Albasa
A daren jiya Litinin ne hukumar lura da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano wato KAROTA ta kwashe kayayyakin ƴan kasuwar sayar da kujeru da kayan katako da ke unguwar Gandun Albasa a nan birnin Kano.
Wani mai sayar da kujeru a wurin ya shaida wa Freedom Radio cewa jami’an KAROTA sun yiwa titin ƙawanya cikin dare tare da kwashe kayayyakin ƴan kasuwar da ke bakin titi suka kuma tafi da su.
‘Yan kasuwar dai sun ce dama hukumar Karota ta basu wa’adin su matsar da kayayyakin su daga bakin titi, kuma suka bi umarnin amma duk da haka sai ‘yan Karotan suka je gurin tare da kwashe kayan.
Alhaji Nasiru Usman Na’ibawa shi ne mai bai wa gwamnan Kano shawara kan hukumar ta Karota yace hukumar na da hurumin aiki a ko ina, musamman tabbatar da cewa masu sana’o’I basu cushe hanyoyin wucewar jama’a ba.
Ya ce bisa al’ada idan hakan ta faru shugabannin kasuwa kan je hukumar don karbar kayan mambobin su amma bisa sharadin daina kasa kaya barkatai a kan titi.
You must be logged in to post a comment Login