Connect with us

Labarai

KAROTA ta zargi wasu matasa da kai wa jami’anta hari tare da kona motar aiki

Published

on

Hukumar Kula da Zirga-zirgar ababen Hawa ta Jihar Kano KAROTA ta zargi wasu fusatattun matasa da kai wa jami’anta hari tare da kona motar aiki a yankin Kwanar Dawaki.

 

Hukumar ta bayyana cewa, hakan ya faru ne biyo bayan wani hatsarin mota da ya afku tsakanin wata babbar motar daukar Kaya da wata motar kirar Sharon.

 

Mataimakin Shugaban Hukumar ta KAROTA, Auwal Shu’aibu Aranposu, ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio ta wayar tarho.

Ya ce, lamarin ya faru ne yayin da jami’an hukumar ke tsaka da gudanar da aikinsu na kula da zirga-zirga ababen hawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!