Labarai
Sojoji sun kama mutane 4 da ake zargi da samar wa yan Boko Haram kayan tallafi

Dakarun rundunar sojin Najeriya, sun kama wasu mutane hudu da ake zargin suna samar wa kungiyar yan Ta’addar Boko Haram kayan tallafi da na aiki a jihohin Borno da Yobe.
Rahotanni sun ce kamen ya biyo bayan wasu hare-hare na musamman da sojoji suka gudanar, inda aka dakile hanyoyin da ake bi wajen kai wa kungiyar kayan da take amfani da su.
Ana zargin mutanen da samar da kayayyakin masarufi da sauran abubuwan da ke taimaka wa kungiyar wajen ci gaba da ayyukanta.
Rundunar sojin ta ce wannan nasara na daga cikin kokarinta na karya hanyoyin samun tallafi ga ‘yan ta’adda da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.
Ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano sauran mutanen da ka iya kasancewa da hannu a wannan aiki.
You must be logged in to post a comment Login