Labarai
Kasar nan tayi asarar sama da megawatt 3000 na wutar lantarki
A kalla sama da megawatt 3000 na wutar lantarki akayi asara a kasar nan sakamakon gobarar da ta tashi dalilin fashewar wani bututun iskar gas a jihar Edo da ya sabba daukewar wutar lantarki a mafi yawan sassan kasar nan.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da ma’aikatar ayyuka wutar lantarki da gidaje ta fitar da yammacin jiya a Abuja.
Ta ce wannan lamari ne ya sanya aka dakatar da tura iskar gas din ta cikin bututun zuwa wasu tashoshin bada wutar lantarkin a kasar nan da suka hadar da Egbin da ke samar da megawatt 1,320 sai kuma Olorunsogo da take samar da MG 676 da kuma Omotosho da ke samar da MG450 da kuma Paras da ke samar da MG60.
Haka kuma ma’aikatar ta yi karin bayani da cewar wannan matsala da aka samu ta fashewar bututun da ke kai iskar gas wadannan tashoshin ya sanya babbar tashar samar da wutar lantarki a kasar nan ta samu matsala da yammacin shekaran jiya Talata.
Haka kuma ma’aikatar ta ne mi afuwar yan Najeriya kan wannan matsala inda ta ce kamfanin tunkudo wutar lantarki TCN da kuma hukumomin da abin ya shafa na aiki tukuru domin ganin an shawo kan matsalar.