Labaran Kano
Kasar Spain ta gayyaci ‘Adama Traore’ cikin tawagar ‘yan wasanta

Daga Anas Muhammad Mande
Kasar Spain ta gayyaci dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Wolverhampton Wanderers da ke kasar Ingila Adama Traore, da ya shiga cikin tawagar ‘yan wasanta a karawar da kasar za ta yi da kasar Jamus da kuma Ukraine.
Adama Traore mai shekara 24, a watan Janairun da ya gabata, ya bayyana cewa kawo yanzu bai yanke shawara kowace kasa zai wakilta ba tsakanin kasar ta Spain da kuma kasar sa ta asali Mali.
A kwanakin baya Spain ta gayyaci Adama Traore don wakiltar ta a fafatawar su da kasar Romania a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, amma bai samu ikon amsa gayyatar ba sakamakon raunin da ya yi.
You must be logged in to post a comment Login