Manyan Labarai
Kashi 99 na masu kai hare-hare ‘yan Najeriya ne – Buratai
Babban hafsan sojan kasar nan Yusuf Tukur Buratai nan bada jimawa za’a kawo karshen matsalar rashin tsaro da kasar nan ke fuskanta, in har ‘yan Najeriya na son hakan.
Yusuf Buratai ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa dake Abuja a dazun nan.
Ka zalika babban hafasan sojan kasar nan ya nunar cewa akasarin kashi 99 cikin 100 wadanda suke kai hare-haren da ake kai wa a sassan kasar nan ‘yan Najeriya, yana mai cewar ana samun nasarori a yaki da ta’addanci a kasar nan.
labarai masu alaka :
Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da hare-haren Sokoto
Yanzu- yanzu : Shugaba Buhari na ganawar sirri da Buratai
Tukur Buratai:jajircewar a faggen daga da sadakarwa sojojin ya kawo cigaban tsaro a Najeriya
A dai ranar Asabar ne ‘yan bindiga suka kashe sojoji 16 da raunata 30 bayan da suka yi musu kwantan-bauna a yankin Shimfida dake karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.
You must be logged in to post a comment Login