Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kashim Shatima ya buɗe Ofishin Gwamna Abba Gida-Gida

Published

on

Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shatima ya bude ofishin Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf dake gidan gwamnati kano

Da yake bude ofishin, wanda gwamnatin jihar Kano ta sabunta, Mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shatima ya jinjinawa Gwamnan Kano bisa ayyukan raya kasa da yake aiwatarwa a jihar Kano.

Kashim Shatima ya zo jihar Kano ne domin halartar jana’izar tsohon shugaban majalisar wakilai ta tarayya Alh.Ghali Umar Na’abba wanda aka yi jana’izarsa da yammacin Laraba 27 ga watan Disamba 2023

Haka kuma Kashim Shatima ya miƙa saƙon ta’aziyya ga gwamnatin Kano da iyalan mamacin a madadin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tunubu inda ya bayyana mutuwar a matsayin babban rashi wanda baza’a iya mantawa da shi ba.

Mataimakin shugaban ƙasar ya sami rakiyar mataimakin shugaban majalisar Dattijai  Barau Jibrin da sanatan Kano ta Kudu Abdurrahman Kawu Sumaila da sauran ƴan majalisar tarayya

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!