Labarai
Kano ta zama ta uku a Najeriya wajen kula da sauyin yanayi

Jihar Kano ta samu matsayi na uku cikin jihohin Najeriya 36 a jadawalin tantance yadda jihohi ke gudanar da harkokin sauyin yanayi na shekarar 2026. Jihar ta samu gagarumin ci gaba daga matsayi na 35 da ta kasance a shekarar 2024, zuwa na huɗu a 2025, kafin ta koma matsayi na uku a sabon jadawalin na shekarar 2026.
Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya ce ci gaban ya samo asali ne daga sauye-sauyen hukumomi da ƙarfafa haɗin gwiwa da aka samu ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf. Hashim ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da jadawalin Subnational Climate Governance Performance Rating and Ranking na shekarar 2026 a Abuja ranar Alhamis.
Ya ce jihar na aiwatar da matakai da suka haɗa da manufar sauyin yanayi da kuma ci gaba da aikin dokar sauyin yanayi. Ya kuma ce shirin dasa bishiyoyi miliyan 10 na daga cikin matakan kare muhalli, bayan da aka raba fiye da miliyan 5.5 na itatuwan dasawa a ƙananan hukumomi 44 a shekarar 2025, tare da amfani da GPS wajen bibiyar wuraren dasawa da kuma yawan bishiyoyin da suka rayu.
Kwamishinan ya ce Kano za ta ƙara mai da hankali kan rage matsalolin ambaliya, zaizayar ƙasa, lalacewar ƙasa, ƙarancin ruwa da gurɓacewar muhalli, tare da ƙarfafa hukumomi da neman kuɗaɗen gudanar da ayyukan sauyin yanayi. Ya ce nasarar jihar ba za ta tsaya ga matsayinta a jadawalin ba, illa za a auna ta ne da irin tasirin manufofin gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Kano.
You must be logged in to post a comment Login