Connect with us

Labarai

Shettima ya isa Saliyo domin taron shugabannin ECOWAS

Published

on

 

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya isa birnin Lungi na kasar Saliyo domin halartar taron shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar ECOWAS karo na 69.

 

An tarbe shi a filin jirgin saman Lungi daga cikin jami’an gwamnatin Saliyo da na Najeriya, ciki har da Mataimakin Shugaban Kasar Saliyo, Dr. Mohamed Jalloh, Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, da wasu manyan jami’an diflomasiyya.

 

Ana sa ran shugabannin kasashen kungiyar za su tattauna batutuwan da suka shafi zaman lafiya, tsaro, bunkasa tattalin arziki da karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen Yammacin Afirka. Rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ce halartar Najeriya na nuna kudurin kasar na ci gaba da taka rawa wajen inganta hadin kan kasashen ECOWAS.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!