Connect with us

Labarai

Katsina: Yan sanda sun ceto mata 2 da aka yi garkuwa da su

Published

on

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Katsina ta  ceto wasu mata biyu da aka yi garkuwa da su tare da daƙile yunƙurin satar Shanu a ƙananan hukumomin Kankia da Charanchi.

 

Hakan  na cikin sanarwar da mai magana da yaun runduna, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar.

 

Sanarwar ta bayyana cewa dakarun rundunar sun yi artabu da ƴan bindiga bayan sun kai hari ƙauyen Jauga da ke Sabon Gida a Ƙaramar Hukumar Kankia, lamarin da ya sa suka tsere zuwa daji tare da barin matan biyu da suka yi garkuwa da su.

 

Matan da aka ceto sun haɗa da Rukayya Yahaya mai shekara 20 da Sahura Abdulhadi mai shekara 22.

 

Rundunar ta ƙara da cewa a wani samame daban, ta daƙile yunƙurin satar shanu da ƴan bindiga suka kai ƙauyen Majen Waya da ke Ƙaramar Hukumar Charanchi bayan musayar wuta da aka yi tsakaninsu da jami’an tsaro.

 

Sanarwar ta ce, babu wanda ya rasa ransa kuma ba a yi nasarar sace ko guda daga cikin shanun ba, yayin da ake ci gaba da farautar ƴan bindigar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!