Connect with us

Labarai

Sojoji sun ceto mutum tara da aka sace tare da dabbobi 56 a Katsina

Published

on

Dakarun Operation FANSAN YAMMA da ke aikin haɗin gwiwa a Arewa maso Yamma sun ceto mutum tara da aka yi garkuwa da su, tare da kwato dabbobi 56 da aka sace, sannan suka kama wani da ake zargi da alaƙa da ‘yan ta’adda a wasu hare-hare daban-daban da suka gudanar a Jihar Katsina.

Mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, yana mai cewa an gudanar da ayyukan ne bisa sahihan bayanan sirri a sassa daban-daban na jihar.

Ya ce dakarun Sector 2 sun ceto mutanen tara da suka haɗa da mata uku, maza huɗu da yara biyu yayin sintirin yaƙi a ƙaramar hukumar Faskari.

Binciken farko ya nuna cewa an yi garkuwa da su ne a ranar 9 ga Yulin 2026 a kan hanyar Tsafe–Kuchere da ke ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.

A cewarsa, mutanen sun bayyana cewa sun samu damar tserewa daga maboyar masu garkuwa bayan waɗanda suka sace su sun yi barci, kafin sojoji su same su tare da ceto su. Yanzu haka suna hannun jami’an tsaro, inda ake shirya haɗa su da iyalansu.

Haka kuma, Danja ya ce dakarun sun dakile yunƙurin wasu ‘yan ta’adda na satar dabbobi a ƙaramar hukumar Bakori.

Ya bayyana cewa bayan samun bayanan sirri, sojojin sun garzaya wurin, inda masu laifin suka buɗe musu wuta. Sai dai saboda ƙarfin wutar da sojojin suka yi amfani da shi, ‘yan ta’addan suka tsere zuwa cikin daji, suka bar dabbobi 56 da suka haɗa da shanu huɗu da tumaki 52.

An ce dabbobin da aka kwato suna hannun sojoji, kuma za a miƙa su ga hukumomin da abin ya shafa.

A wani samame na daban a ƙaramar hukumar Danmusa, dakarun sun kama wani da ake zargi da alaƙa da ayyukan ta’addanci.

Mai magana da yawun ya ce binciken farko kan kayayyakin da aka samu tare da wanda ake zargin ya nuna akwai alamun alaƙarsa da ayyukan ta’addanci, kuma yana ci gaba da kasancewa a tsare domin zurfafa bincike.

A ƙarshe, kwamandan rundunar Operation FANSAN YAMMA ya yaba wa dakarun bisa ƙwarewa, jajircewa da kuma taka-tsantsan da suka nuna, yana mai jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da hare-haren da suka dogara da bayanan sirri tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro da al’umma, har sai an shawo kan ta’addanci da sauran laifuka a yankin Arewa maso Yamma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!