Labarai
Gwamnati ta samar da kashi 90 na duk magunguna da kayan aiki a asibitoci- Pharm. Ghali Sule

Gwamnatin jihar Kano ta ce an samu sama da kashi casa’in cikin ɗari na dukkan magunguna da kayan aikin da marasa lafiya ke buƙata a asibitocin gwamnati, sakamakon ƙoƙarin da ta yi wajen inganta harkokin lafiya da zuba jari a fannin.
Shugaban Hukumar samar da magunguna da kayan aikin lafiya na Kano, Pharm. Ghali Sule, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai, domin bayyana nasarorin da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta samu a fannin lafiya, a cikin shekaru uku.
Pharm. Ghali Sule, ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin za ta ci gaba da saka hannun jari a fannin lafiya domin tabbatar da cewa al’ummar Kano na samun ingantaccen kulawar lafiya a dukkan asibitocin gwamnati da ke yankunan birni da karkara.
Pharm. Ghali, ya ce, gwamnatin Kano ta samu gagarumar nasara wajen inganta ayyukan kiwon lafiya, inda ta tabbatar da wadatar magunguna da kayan aikin jinya a mafi yawan asibitocin gwamnati domin baiwa al’umma ingantaccen kulawa.
You must be logged in to post a comment Login