Labarai
Gwamnatin tarayya na shirin sake kwaso yan Najeriya da Afirka ta Kudu

Ma’aikatar harkokin wajen ta Najeriya, ta bayyana cewa jirgin na biyar da ake amfani da shi wajen kwaso ‘yan Najeriya daga Afirka ta Kudu zai tashi daga Johannesburg da ƙarfe 1:30 na daren Larabar makon nan 2026.
Mai magana da yawun ma’aikatar Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.
Sanarwar ta ce jirgin na kamfanin Air Peace zai ɗakko ‘yan Najeriya 315 da suka nuna sha’awar koma wa gida sakamakon hare-haren ƙyamar baƙi da matsalolin tsaro a wasu sassan Afirka ta Kudu, da ake sa ran jirgin zai sauka a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas da misalin ƙarfe 6:30 na safiya.
Gwamnatin Tarayya ta ce tun bayan fara aikin kwaso ‘yan ƙasar a ranar 11 ga Yuni, ta gudanar da jigilar mutane sau huɗu inda ta dawo da ‘yan Najeriya 1,141 gida.
Haka kuma, wasu mutum 66 sun dawo ta hanyar wani kamfani mai zaman kansa, yayin da Air Peace ya sake taimaka wa wajen dawo da wasu mutane 39.
You must be logged in to post a comment Login