Labarai
KCSF ta karyata rahoton da yake yawo na dakatar da shugabancin kungiyar
Kwamatin amintattuna na gamayyar kungiyoyin kishin al’umma a nan jihar Kano Civil Society Forum, ya ce zai yi duk mai yuwuwa wajen ganin an ci gaba da samun hadin kai tsakanin kungiyoyin kishin al’umma a Jihar.
Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren kwamatin, Alhaji Hamisu Isah Sharifai ya fitar ga manema labarai.
Sanarwar ta ce, hakan ya biyo bayan rahotonnin da kwamatin ya samu kan cire shugaban gamayyar kungiyoyin Ibrahim Wayya da wasu ke ikirarin yi.
Ta cikin sanarwar kwamatin ya kuma ce har yanzu shugabannin kungiyar sune halastattun shugabanni.
Sai dai Jim kadan bayan fitar wannan sanarwa shugaban gamayyar kungiyoyin da ake ikirarin cirewa Ibrahim Wayya ya cewa wadanda suka sauke shugabannin basu da hurumin hakan, da suke zargin akwai siyasa a cikin lamarin.
Wayya ya ce kowacce kungiya tana da tsare-tsaren da take bi wajen zaban shugabanninta, da Kuma sauya su, saboda haka wancan rahoton bashi da tushe ko makama.
Rahoton: Abubakar Tijjani Rabi’u
You must be logged in to post a comment Login