Connect with us

Labarai

Sojoji sun ceto mutane 4 da aka yi garkuwa da su tare da marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar

Published

on

Dakarun sojin Najeriya sun ceto sauran mutane hudu da aka yi garkuwa da su tare da marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya a Jihar Katsina.

 

Wannan na cikin sanarwar da Kwamishinan Tsaro na Jihar Katsina Dakta Nasir Mu’azu, ya fitar a yau Laraba.

 

Sanarwar ta ce an ceto Musa Yakuba mai shekaru 62, Alhaji Sa’adu Dayi mai shekaru 68, Mukhtar Danja mai shekaru 36 da Salisu Danja mai shekaru 50 yayin da sojoji ke ci gaba da gudanar da farmaki domin kamo shugaban ‘yan bindiga Kachalla Muhammadu Fulani da mabiyan sa.

 

Sanarwar ta bayyana cewa jami’an lafiya sun kula da mutanen bayan an ceto su sakamakon raunukan harbin bindiga da suka samu a lokacin da suke hannun masu garkuwa da mutane.

 

Sanarwar ta ce an riga an ceto matar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar, yayin da mutanen da aka ceto suke cikin wadanda aka gani tare da shi a wani hoto kafin rasuwarsa.

 

Dakta Nasir Mu’azu ya ce jami’an tsaro na ci gaba da bin sahun Kachalla Muhammadu Fulani da sauran masu aikata laifuka, tare da jaddada cewa farmakin zai ci gaba har sai an kamo wadanda ke da hannu a ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!