Kiwon Lafiya
Kemi Adesun:kasafin bana zai fi maida hankali wajen bunkasa manyan ayyuka
Gwamatin tarayya ta ce kasafin bana zai fi mida hankali wajen bunkasa manyan ayyuka a fadin kasar nan musamman ma wajen ganin an karasa ayyukan gine-gine da aka faro.
Ministar Kudi Kemi Adeosun ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa mai dauke da sa-hannun mashawarcinta na musamman kan harkokin yada labarai Oluyinka Akintunde.
Misis Kemi Adeosun wadda ta wakilci mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a wajen gabatar da wata Makala, a kwalejin horas hafoshin tsaro NDC a Abuja karo na 26, ta ce gwamnatin tarayya za ta iya kokarinta wajen tabbatar da ayyukan duk kuwa da karatowar babban zaben kasa.
Ta kuma jaddada kudurin gwamnatin tarayya na kawo sauyin da zai ciyar da kasar nan gaba musamman batun samar da aikin yi ga ‘yan kasa domin bunkasa tattalin arzikin kasar baki-daya.
Taken Makalar da ta gabatar a madadin mataimakin shugaban kasa shi ne Harkokin tattalin arziki da kuma Tsaron kasa, tana mai cewar kyautatuwa da kuma bankasar tattalin arziki su ne ginshikin cimma ko wane muradi a rayuwa.
Har ila yau ta cikin makalar, mataimakin shugaban kasa ya tabbatar da yakininsa na cewa tattalin arzikin kasa zai bunkasa da kashe uku a bana