Ƙetare
An saka dokar hana fita sakamakon ɓarkewar zanga-zanga a yayin zaɓen shugaba kasa a Tanzaniya

Rundunar yan sanda a ƙasar Tanzania sun saka dokar hana fita a fadin ƙasar baki daya biyo bayan zanga-zangar da ta ɓarke yayin zaɓen shugaban ƙasa da ya rikiɗe zuwa rikici da fadace-fadace a wasu sassan ƙasar.
Rahotanni sun nuna cewa, zanga-zangar ta ɓarke ne a birnin Dar es Salaam da wasu garuruwa yayin da jama’a ke nuna rashin jin daɗi kan yadda ake gudanar da zaɓen shugaban ƙasar.
Masu zanga-zangar sun yi zargin cewa akwai son kai da rashin gaskiya a tsarin zaɓen, tare da neman gwamnati ta gyara tsarin zaɓe da kuma ba kowa damar faɗar albarkacin baki.
Jami’an tsaro, sun ce an sanya dokar ne domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Sai dai wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun bayyana damuwa tare da bayyana hakan a matsayin tauye ’yancin jama’a musamman a lokacin da ake jiran sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.
You must be logged in to post a comment Login