Connect with us

Labarai

KNUPDA ta bukaci mazauna Kano su mallaki izinin gini don kauce wa iftila’in rusau

Published

on

Hukumar Tsara Birane da ta Jihar Kano (KNUPDA) ta bukaci mazauna jihar da su tabbatar sun mallaki izinin gini kafin fara duk wani aikin gini, tana mai jaddada cewa bin ka’idojin gine-gine da aka amince da su na da matukar muhimmanci wajen dakile rugujewar gine-gine da kare rayuka da dukiyoyi.

Wannan na cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulda da Jama’a ta KNUPDA, Bahijja Malam Kabara, ta fitar, inda ta ce Mukaddashin Daraktan Gudanarwa na hukumar, Tpl. Nura Maude, ya yi wannan kira yayin da yake duba gine-ginen da suka ruguje a wasu sassan Jihar Kano, ciki har da Karamar Hukumar Tarauni da Kurna da ke Karamar Hukumar Fagge. Wadannan hadurran sun yi sanadin asarar rayuka, jikkatar wasu mutane da kuma lalata dukiyoyi.

Mukaddashin Daraktan Gudanarwa na KNUPDA, Tpl. Nura Maude, ya bayyana cewa samun izinin gini na daga cikin muhimman matakan tabbatar da tsaro, domin yana tabbatar da cewa gine-ginen da ake shirin ginawa sun cika ka’idojin tsara birane, tsarin gini da kuma muhalli da aka amince da su.

Ya kuma gargadi masu gidaje da masu amfani da gine-gine cewa rashin bin ka’idojin gini na iya jefa masu gidaje, mazauna gine-gine da kuma al’ummomin da ke makwabtaka da su cikin babban hadari, wanda zai iya haifar da jikkata, asarar rayuka da kuma dimbin asarar dukiyoyi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!