Labarai
Tsofaffin Sojoji sun gudanar da zanga-zanga a Abuja

Wasu tsoffin Sojojin kasar nan, sun gudanar da zanga-zanga a birnin tarayya Abuja, bayan da jami’an tsaro suka hanasu shiga harabar Ma’aikatar Tsaro domin neman a aiwatar da karin kudi a fanshon su.
Rahotonni sun bayyana cewa, tsoffin sojojin sun taru a wani fili da ke kusa da ma’aikatar da tsakar ranar yau Laraba dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce da ke bayyana bukatunsu.
Sai dai, yayin da suke kokarin isa babbar kofar ma’aikatar, sai sojoji suka hana su shiga.
Jami’an ’yan sanda da na Hukumar tsaro ta Civil Defence ma sun bada gudunmawar tare hanyoyin da suke kusa da ma’aikatar.
Amma daga bisani, tsoffin sojojin suka koma tsakiyar hanya, inda suka yi wa manema labarai bayani kan korafinsu.
You must be logged in to post a comment Login