Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ko Gwamnatin Kano za ta mayar da marayun Nassarawa zuwa Gaya?

Published

on

A ranar Litinin ne wani labari ya karaɗe kafafen sada zumunta da ke cewar, an fara kwashe yaran da ke gidan yara na Nassarawa zuwa sabon gidan marayu na garin Gaya.

An yi ta yaɗa cewa, Gwamnatin Kano ta shirya cefanar da gidan, cikin jerin kadarorin Gwamnati da ake zargin tana sayarwa.

Wasu rahotonni sun ce, jami’an ma’aikatar mata da ƙananan yara ta Kano da jami’an tsaro ne ke ɗibar yaran.

Me ya ke faruwa?

Da jin wannan labari, Freedom Radio ta garzaya gidan marayun na Nassarawa.

Kuma ta iske motar ƴan sanda guda ɗaya, sannan yara suna cin abinci, kuma an basu sabbin takalma.

Wata majiya a gidan ta shaida mana cewa, babu wani abu makamancin wannan labarin da ya faru.

Daga nan muka garzaya ma’aikatar mata da ƙananan yara ta Kano.

Karin labarai:

Siyasar Kano: PDP ta gargaɗi Ganduje kan cefanar da kadarorin gwamnati

Bai dace a dinga cefanar da wuraren wasanni ba a Kano- Masanin motsa jiki

Kwamishiniyar ma’aikatar Dakta Zahra’u Muhammad Umar ta ce, ba sayar da gidan marayun za a ayi ba.

A cewar ta, hukumar kula da kamfanonin Inshora ta ƙasa NDIC ce ta gina wa gwamnatin Kano gidan marayu sabo a garin Gaya.

Shi ne, ma’aikatar ta ɗebi wasu yara ƴan kaɗan masu wayo, da basu kai mutum goma ba, domin sauya musu matsuguni zuwa can.

Ta ce, babu sanin Gwamna Ganduje aciki, ma’aikatar ce ta fara yin gwaji domin cin gajiyar sabon gidan marayun na gaya wanda ta ko ina ya kere na Nassarawa.

Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayin bude sabon gidan marayu a garin Gaya.

Kwamishiniyar ta ce, ya kamata masu yaɗa labarin cewa an cefanar da gidan marayun su ji tsoron Allah su riƙa bincike.

Ko akwai shirin za a ci gaba da ɗiban yaran sannu a hankali ana sauya musu matsuguni zuwa Gaya?

Sai kwamishiniyar ta ce, babu wannan shirin a ƙasa, wannan ma gwaji ne kawai suka yi.

Yaushe aka buɗe gidan marayu a Gaya?

A watan Oktoban shekarar 2020 da ta gabata ne, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya buɗe gidan, bayan da hukumar NDIC ta gina ta kuma miƙa wa Gwamnatin Kano.

Yayin bikin buɗewar shugaban hukumar NDIC ya ce, ginin na cikin ayyukan da hukumar ke yi, domin bunƙasa rayuwar al’umma.

Ya kuma ce, an kashe kuɗi sama da miliyan 51 wajen gina gidan.

Jami’an Gwamnatin Kano da dama ne suka halarci bikin buɗewar.

Ku kalli hotunan bikin buɗe sabon gidan marayu na gaya a ƙasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!