Kimiyya
Ko kun san haɗarin kamuwa da lalurar mantuwa?
Ƙwararren likitan ƙwaƙwalwa a asibitin Aminu Kano ya ce lalurar mantuwa guda ce daga cikin cututtuka masu saurin hallaka ɗan adam.
Dakta Aminu Shehu na sashin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa a asibitin Aminu Kano ne ya sanar da hakan a zantawar sa da Freedom Rdio.
“Lalurar ƙwalƙwalwa na samuwa ne ta hanyar kamuwa da cutar hawan jini, shanyewar barin jiki da kuma sauran cututtukan da kan shafi ƙwaƙwalwa su sanya mata rauni” in ji Dakta Aminu.
Likitan ya ce, a yanzu adadin masu kamuwa da lalurar mantuwa na ƙaruwa, dalilin yadda ake tursasawa ƙwaƙalwa ɗaukan abinda yafi ƙarfin ta.
“Lalurar mantuwa a yanzu ana samun ta akan masu ƙanana da matsakaitan shekaru, saɓanin lokacin baya ana ganin cutar ga waɗanda suka tsufa ko kuma shekarun su suka fara nisa” a cewar likitan.
Alamomin kamuwa da lalurar mantuwa:
“Akan gane alamun kamuwa da lalurar mantuwa ta hanyar rashin tuna wasu abubuwa da suka shuɗe komai muhimmancin su, a wasu lokutan ma masu fama da cutar suna iya manta kan su, ko makusantan su” Dakta Aminu ya faɗa.
Dakta Aminu Shehu ya kuma ce, shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na haifar da lalurar, sai dai ana iya dacen warkewa idan da ƙananun shekaru, saɓanin waɗanda shekarun su suka nisa.
You must be logged in to post a comment Login