Labaran Kano
Ko kun san mara lafiyar da ba a sani ba?
Kungiyar likitoci ta kasa reshen jihar Kano ta bayyana cewa, an fara gudanar da bikin makon likitoci ne sakamakon yadda ake mantawa da wasu cutuka da suka gabata da nufin cigaba da tunawa das u da kuma irin gudunmawar da likitoci ke bayarwa.
Shugaban kungiyar likitocin reshen Kano Dr. Sunusi Muhammad Bala, ne ya bayyana hakan ta cikin shirin’’Duniyar mu a Yau na nan Freedom Radio, da ya mayar da hankali kan kan bikin makon likitocin da aka kwashe shekaru 60 ana gudanarwa duk shekara.
Ya kuma ce taken bikin na bana da aka kira da ‘‘Maras lafiyar da ba a sani ba’’’ abun ya zo a kan gaba, la’akari da irin yadda ake baiwa mutanen da ba a san su ba taimakon gaggawa kafin a kai ga gano ‘yan uwansu.
Da yake tsokaci ta cikin shirin, tsohon sakataren kungiyar ma’aikatan jinya na sashen wadanda ke bukatar kulawar gaggawa reshen jihar Kano, Munnir Habibu Bello, cewa ya yi babban kalubalen da suke fuskanta shi ne yadda ake kawo musu marasa lafiyar da ba a san danginsu ba, inda a wasu lokutan ake kawo wadanda ba sa cikin hayyacinsu.
Haka kuma ya kara da cewa idan an kawo musu maras lafiyar da ya gamu da tsautsayi sukan yi kokarin gano wata shaida da ake gane daga inda ya fito lokacin da ake bashi taimakon gaggawa.