Siyasa
Kofa ya koma Kasuwa bayan faduwa a zabe
Kasa da mako guda, bayan faduwar tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji, na jam’iyyar APC Abdulmumin Jibril Kofa, ya ce ya koma kasuwanci don cigaba da gudanar da harkokin sa na yau da kullum.
Abdulmumin Jibril Kofa, ya bayyana hakan ne, a shafin sa na dandalin sada zamunta na Facebook, inda ya wallafa hoton sa da na dan sa Abdulrahman Majidadi, sannan ya kara da cewa
“Mun koma harkokin kasuwanci, zan duba na gani shin har yanzu da sauran kasuwanci a tartare dani, watakila a dace na yi kasuwa sosai tare da samun kudade da dama”.
Haka kuma tsohon dan Majalisar, ya ce dan nasa ya bashi shawarwari, kuma zaman nasu ya yi armashi, inda ya wallafa hotuna, da kuma hoto mai motsi wato Bidiyo a yayin komawar tasa zuwa ofishin kasuwancin sa.
Labarai masu alaka:
Majalisar wakilai ta janye dakatarwar da ta yiwa Abdulmumin Jibrin kofa
A baya-bayan dai, dan Majalisar ya yi fama da rikice -rikicen cikin gida a jam’iyyar sa, wanda ya janyo masa dakatarwa a majalisa.
Har ila yau, bayan dawowar Abdulmumin Kofa daga dakatarwar da akayi masa, ya samu sabani da jagororin jam’iyyar na jihar Kano.
Al’umma na ganin hakanne ya sanya aka dauki hotunan bidiyon sa yayin da yake baiwa shugaban jam’iyyar na jiha Abdullahi Abbas, hakuri, lokacin da ya durkusa masa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, dake nan Kano.
Sai dai duk da hakan ya yin zaben cike gurbi daya gudana a Asabar din makon jiya, dan takarar ya sha Kaye a hannun abokin karawar sa na jam’iyyar hamayya ta PDP Ali Datti Yako.
Labarai Masu Alaka:
Mun samu rahoton aikata ba daidai ba a wasu mazabu-Abdulmumini Jibrin.