Labarai
Kome yasa akewa kananan yara fyade
Fyade wani nau’i ne na cin zarafin bil adama walau mace ko namiji sai dai galibi yafi faruwa kan jinsin mata, ta hanyar tursasasu yin lalatadasu, wanda sanadiyar hakan yake zubar musu mutunci da kuma kima da su ke dashi, a wasu lokutan ma yakan kai har ga rasa rayuka sakamakon rauni.
Bincike yayi nuni da cewa karuwar matsalar fyade a wannan lokaci ya zamo tamkar ruwan dare ne gama duniya, inda a kusan kullum yanzu mutum ya saurari kafar yada labarai ba zai rasa jin korafi kan fyade ba.
Wata yarinya ‘yar shekaru 5 da rabi da ta gamu da Fyade, a Nageriya ta bayyanawa Freedom Radio yadda wani mutum ya yi nasarar yi mata fyade, tare kuma da yi mata barazana idan taki amincewa da shi.
Babban abin tausayin shine yadda yarinyar da karancin shekarun ta take da burin ganin an yi mata adalci ta hanyar hukunta mutumin da ya yi mata wannan aika-aika bata ji ba bata gani ba, ba kuma tare da tayi shigar da ta nuna tsaraici ko kwarkwasar da a iya cewa ita ta janyo hankalin sa ba.
Masana dai sun bayyana fyade a matsayin wata hanya ta biyan bukatar mutum, ba tare da amincewar wanda zai biya bukatar da shi ba, ta hnayar tilastawa, ko kuma barazana ko yaudara wadda shine da masu wannan dabi’a suka fi bi wajen yiwa yara kananan fyaden.
Wani dan gwagwarmaya zai bi kadin yadda aka yi wa yarinya fyade
Mata ‘yan kasa da shekaru 9 aka fi yiwa Fyade a Najeriya
Dama can akwai dabi’ar Fyade to amma a wannan lokaci ta kara Kamari ta yadda abin ke neman ya gagari kundila, inda kuma alamu ke nuna cewa mahukunta basu da niyyar daukar wani mataki mai tsauri kan masu wannan dabi’a don su hankalta.
Kasar Indiya dai na cikin kasashen da ke kan gaba da matansu suka fi fama da bala’in fyade, amma abin yanzu a iya cewa ya shigo kasar nan gadan-gadan, ta yadda wasu ke ganin sa a matsayin sakacin matan, a cewar su, su suke yin shigar da ba ta dace ba da ke janyo hankalin masu aikata fyaden a kasu.
Sai dai shugaban sashen kula da wadanda suka gamu da ibtila’in fyade mai taken ‘Waraka’ da ke asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke nan Kano Malam Abba Bello ya musanta wannan batu yana mai cewa sama da kaso 70 na wadanda ake yiwa fyade kananan yara ne ‘yan kasa da shekaru 9 wadanda basu da wasu hallitu da ka iya janyo hankalin masu aikata fyaden.
Ita ma da ta ke zantawa da Freedom Radio Mataimakiyar Shugabar kungiyar Kwararrun lauyoyi mata ta kasa FIDA Barista Nibras Tahir Jalalain ta ce wannan babban bala’I ne da ke fuskantar mata, a duniya baki daya, ba ga manya ba baga yara ba.
Haka kuma ta ce hakan na faruwa ba a iya yankunan da mata kedaura zani ko a turai da suke sa wanda ko a indiya da suke sanya Sari ko kuma a kasashen larabawa da suke sanya jallabiyya ba, a don haka bashi da wata alaka da shigar da mace ta yi.
Tana mai cewa hukuncin kisa da tarar naira dubu dari biyu biyan diyya ga wadda aka yiwa fyade shine hukuncin da doka ta tanada a kasar nan amma abin takaicin shine ba a daukar matakin.
Barista Nibras ta kuma ce baya ga bala’in na Fyade, abinda ke kara tayar da hankalin wadanda aka yiwa fyaden shine tsana da tsangwama da ake nuna musu, ba tare da la’akari da wanda ya aikata laifin ba.
Ta yadda a wasu lokutan sai dai matan su kasha kansu ko su bar garin don samun mijin aure, amma shi wanda ya aikata laifin na nan yana yawon sa cikin jin dadi ba kuma tare da wata matsala ba.
Idan aka yi maganar fyade dai ba iya mata ya ke shafa ba, har ma da yara maza a wasu lokutan ma har da manya a don haka aiki ne na maza da mata a hada hannu don yaki da masu aikata wannan dabi’a, kasancewar tana iya shafar kowa
You must be logged in to post a comment Login