Labarai
Kotu ta bada umarnin aikewa da abduljabbar Kabara asibitin Dawanau
Babbar kotun shariar musulinci dake ƙofar kudu karkashin mai sharia Ibrahim Sarki Yola ta bada umarnin a kai malam Abduljabbar zuwa asibitin Dawanau domin a duba lafiyar ƙwaƙwalwarsa da kuma kunnansa.
A zaman kotun na yau, kotun ta bada umarnin a karantawa malam Abduljabbar laifukan da ake tuhumarsa amma yaƙi amsawa.
Haka kuma lauyoyinsa sun ƙiyin martani kan tuhume tuhumen da ake masa a zaman na yau.
Mai sharia Sarki Yola ya bada umarnin a rubuta kwafin shari’ar baki ɗaya a baiwa lauyoyin Abduljabbar ɗin a nan take.
Sarki Yola na cewa koda lauyoyin malam Abduljabbar Kabara sun ɗaukaka ƙara ba za ta dakatar da ci gaba da shari’arsa ba.
Haka kuma ya sanya ranar 16 ga watan da muke ciki domin ci gaba da shari’ar.
You must be logged in to post a comment Login