Manyan Labarai
Kotu a Kano ta aike da Kansila gidan gyaran hali
Kotun majistret mai zamanta a nan Kano ta aike da kansilan mazabar Bachirawa a karamar Hukumar Ungogo gidan yari saboda dokan wani matashi.
A makon da ya gabata ne dai ‘Yansanda ne dai suka gurfanar da kansilan Hon. Saddik Rabiu Zubairu, a kan zargin kansilan da lefin kutse da sanadin rauni da kuma keta alfarmar dan adam.
Ana dai zargin kansilan na Bachirawa mai suna Saddiku Rabiu da ya balle kofar shagon wani matashi mai suna Auwalu mai Wake da yi masa dukan daga karshe kuma su ka hadu shi da wasu kartai saboda mai waken yace wa kansila ya ci taliyar karshe.
Ka zalika a ranar Juma’ar da ta gabata ‘yansanda su ka gurfanar da su a gaban kotu amma da yake kotu wuri ne na adalci nan take mai shari’a Hajiya Talatu makama ta bayar da belin kansila a ranar Juma’ar a ka kuma sanya yau Litinin domin a dawo kotu a ci gaba da shari’a.
Amma dai Kansila bai samu damar halartar kotun ba sai bayan karfe 11 lokacin kuwa har an kirawo shari’ar sai dai a lokacin kansila bai karaso kotun ba.
Mai gabatar da kara ta roki kotun da ta karya belin tunda dai kotu ba ta jiran kowa sai dai a jira kotu kuma nan take kotun ta janye belin.
Yayin da kansilan ya bayyana a kotun ya nemi a yi masa hanzari kasancewar an wayi gari lauyansa baya jin dadi kuma shi ne ya kai lauyan asibiti sai dai kotun tayi watsi da rokon.
Wakilin mu na kotu da ‘yan snada ya rawaito cewar, mai kara Auwalu mai Wake ya bayyanawa kotun cewar, bayan Kansila akwai wani dogarin kansilan mai suna Ado Babba da kuma kanin kansila Hassan Rabi’u amma kuma kansilan kawai a ka gurfanar
Sai dai rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano na cigaba da bincike ya yin da ta sami mutum 2 da laifi ya yin da alkalin ya ce kotu abin da yake gaban ta shi take amfani da shi.
You must be logged in to post a comment Login