Labarai
Kotu : An yanke wa wasu matasa hukuncin dauri a Kano
Babbar Kotun Jihar Kano mai zamanta a sakatariyar Audu Bako karkashin jagorancin mai sharia Aishatu Rabi’u Danlami, ta zartarwa wasu matasa guda uku hukuncin dauri bayan samunsu da laifin fashi da makami.
Matasan da suka hada da Abba Nuhu dake zaune a Unguwar Sharada Kwanar Ganduje, sai Abdulfatah Murtala dake Dorayi karshen Waya mai shekaru 18, da kuma Abdullahi Musa shi ma daga gidan Dakali karshen Waya.
Mai gabatar da kara lauyan gwamnati Muktar Salihu, ya gabatar da shaidu guda biyu, an kuma yanke wa mai laifi na farko Abba Nuhu hukuncin daurin shekaru 14, bisa samunsa da laifin fashi da makami, sai kuma barazana da ya yi wa mutane aka yanke ma sa shekaru bakwai wanda hukuncin ya kama shekaru 21 a gidan gyaran hali.
Mai laifi na biyu Abdulfatah Murtala an zartar ma sa da hukuncin daurin shekaru 14 bisa kokarin fashi da makami.
Zamba Cikin Aminci: Shugaban KAROTA zai gurfana a gaban kotu
Yajin aiki: Dalilan da suka sanya NLC ta yi watsi da umarnin kotu
A shirye nake na bayyana a gaban kotu – Baffa Babba
Mai laifi na uku Abdullahi Musa kuwa an yanke masa hukuncin daurin shekaru 14 bisa laifin kokarin aikata fashi da makami.
Wakilinmu na Kotu Bashir Muhammad Inuwa ya rawaito cewa mai shari’a Aishatu Rabiu Danlami ta ce ta daure su ba tare da zabin tara ba, bayan da mai gabatar da kara ya gabatar da shaidun da suka gamsar da kotu.
You must be logged in to post a comment Login