Labarai
Kotu ta ɗage saurarar ƙarar gwamnatin tarayya da ƙungiyar NARD
Kotun ma’aikata da ke zaman ta a Abuja ta sanya ranar 15 ga watan Satumbar 15 a matsayin ranar da za ta ci gaba da saurar ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar gaban ta kan kungiyar likitoci masu neman ƙwarewa.
Idan za a iya tunawa lokacin da gwamnatin tarayya ta shigar da ƙara gaban kotun, mai shari’a John Targema ya aikewa da kungiyar sammaci.
Har ma ya buƙaci ƙungiyar ta bayyana gaban kotun, don ba da ba’asi kan ƙin amincewa da umarnin gwamnati na rashin biyan su albashi alhalin suna yajin aiki.
Matuƙar ba ku yi aiki ba, ba za mu biya ku albashi ba – Gwamnatin tarayya ga ƙungiyar NARD
Sai dai mai shari’a Targema ta ɗage saurarar ƙarar zuwa ranar 15 ga watan Satumba, domin sauraron buƙatar kowanne bangare.
Tun a ranar 2 ga watan Agustan da muke ciki ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa NARD ta fara yajin aikin, lamarin da ya sanya gwamnatin tarayya ta ce ba za ta ci gaba da biyan su albashi ba, alhalin suna yajin aiki.