Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta bai wa Abduljabbar damar fitar da kuɗi daga asusunsa na banki

Published

on

Kotu ta umarci jami’an gidan gyaran hali da su bar Malam Abduljabbar Nasiru Kabara ya sanya hannu domin fitar da kuɗi daga asusunsa na banki da zai ci gaba da ciyar da iyalansa.

A yau Alhamis kotun shari’ar Muslunci da ke Ƙofar Kudu a nan Kano ta ci gaba da sauraron shari’ar Malam Abduljabbar Nasir Kabara.

Yayin zaman kotun na yau an gabatar da shaida na uku Sufeto Muhd Kabiru daga Shalkwatar ƴan sanda ɗaya daga cikin waɗanda suka yi bincike a kan tuhumar da ake yiwa malamin.

Saidai Abduljabbar ya soki shaidar bayan da yayi masa tambayoyi, sannan ya roƙi kotu ta yi watsi da abin da shaidar ya faɗa.

Labarai masu alaƙa:

Gwamnati zata sayo wa Abduljabbar Sahihul Bukhari da Muslim

Shari’ar Abduljabbar: Lauyoyin Gwamnati sun ci gaba da gabatar da shaidu a gaban kotu

A nan ne lauyan mai kariya AO Muhd SAN ya roƙi kotu ta sanya jami’an gidan gyaran hali su bai wa Abduljabbar damar sanya hannu domin fitar da kuɗi daga asusunsa na baki, don ciyar da iyalansa.

Lauyan ya kuma nemi kotu ta bada belin Malamin sannan ta sanya sati uku masu zuwa domin ci gaba da shari’ar.

Bayan wannan lauyan ya kuma nemi a basu kwafin shari’ar da basu da ita.

Sai dai mai gabatar da ƙara lauyan Gwamnati Surajo Sa’ida SAN ya yi suka, inda ya ce, kamata yayi lauyan ya roƙon a jingine hukuncin da kotun ta yi a baya na zata riƙa zama duk sati biyu.

 

Bayan sauraron ɓangarorin biyu mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya amince da buƙatar lauyan Abduljabbar kan sanya hannu don fitar da kuɗi daga asusunsa.

Amma batun bayar da beli alƙali ya ce kotu na tsoron husuma idan ta bayar, amma nan gaba zata duba yiwuwar hakan matuƙar ba zai jawo fitina.

Dangane da shaidar Sufeto Muhd Kabiru kuwa, alƙalin ya ce, yanzu kotu ta ɓoye ra’ayinta a kai, zata bayyana a yayin hukuncinta na ƙarshe.

Wakilinmu na kotu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim ya rawaito cewa an ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Disambar da muke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!