Kasuwanci
Kotu ta dakatar da bankin CBN daga cire harajin hada-hadar kudade
Babbar kotun tarayya dake zamanta a Awka dake jihar Anambra ta bayyana sabon tsarin babban bankin kasa CBN na hana tafiya da kudade wato (Cashless Policy) a matsayin musgunawa al’umma.
CBN dai ya aiwatar da tsarin ne a jihohi 6 tare da birnin tarayya Abuja inda abokan cinikayyar bankuna ke kokawa kan yawan cajinsu kudaden a kowace hada-hada.
Wannan ya biyo bayan karar da wani masanin shari’a a jihar ya shigar a gaban kotu ya na kalubalantar sabon tsarin na CBN yadda ya sabawa sashi na 42 a kundin tsarin mulkin kasar nan.
A na shi bangaren, Lauya mai kare babban bankin Jackson Iragunima ya ce an fito da sabon tsarin ne don saukakawa al’umma bawai don a musguna musu ba.
You must be logged in to post a comment Login