Labarai
Kotu ta dakatar da shugabancin jam’iyyar APC na mazaɓar Ganduje
Babbar kotun tarayya da ke Kano ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Abdullahi Liman, ta dakatar da shugabancin jam’iyyar APC na mazaɓar Ganduje daga ɗaukar kowane irin mataki ko aiwatar da wani taro wanda ya shafi aikace-aikacen jam’iyyar har zuwa lokacin sauraron wannan shari’a.
Hakan ya biyo bayan wata ƙara da tsohon gwamnan Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya shigar ya na karar Haladu Gwanjo da Muhammad Baita da Malami mai AC da kuma rundunar yansanda.
Sauran waɗanda Gandujen ya yi ƙara sun hadar da kwamishinan ƴan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya da babban sifeton ƴan sanda da kuma hukumar Civil Defence.
Dakta Ganduje, ya roƙi kotun da ta dakatar da wadanda ake kara daga aiwatar da dukkanin wani abu wanda ya shafi wannan shari’a.
Da yake bayyana ra’ayin kotun Justice Liman ya ayyana cewar shugabancin jam iyyar APC na mazabar Ganduje da yan korensu da kuma dukkan hukumomin da akayi kara tare da Haladu Gwanjo da Malami mai AC kada wani yayi wani yunkuri akan batun da ya ahafi wannan shari’a.
Kotun ta ayyana cewar ta dakatar da kowane bangare daga yin wani yunkuri har zuwa ranar 30 ga wata dan sauraron kowane bangare.
You must be logged in to post a comment Login