Connect with us

Labarai

Kotu ta daure guda cikin jagororin ISWAP a Najeriya shekaru 20

Published

on

Wata babbar kotu da ke birnin tarayya Abuja, ta yanke wa ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar yan ta’adda ta ISWAP da kotun ta same shi da laifin kitsa kai hari a wurare da dama a jihar Kano hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari.

Kotun ta kama Hussaini Isma’ila da laifukan da ake zarginsa da aikatawa na kai hare hare a sassa daban daban na jihar Kano, bayan da hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar da shi.

Kotun ta kama Hussaini wanda aka fi sani da maitangaran da kai hari shelkwatar rundunar yan sandan Kano da ke Bompai a shekarar 2012, da wasu ofisoshin yansanda da ke unguwanni Kabuga da unguwa uku da na kasuwar waya da Farm centre, inda mutanen da dama suka mutu, wasu suka jikkata.

An fara shariar ne tun bayan kama shi a ranar 31 watan Agustan 2017 a garin tsamiya babba da ke ƙaramar hukumar Gezawa a Kano.

Sai ai shariar ta fuskanci jinkiri saboda ɗaukaka ƙara da kuma sharia cikin sharia da aka yi ta yi kan wasu laifukan da ake zargin ya aikata.

Hukumar tsaro ta DSS da ta gurfanar da shi ta gabatar da shaidu biyar waɗanda ake ganin sun gamsar da alkalin, ciki har da mutanen da suka shaida kai hare haren.

Tun da farko dai wanda ake zargin ya musanta tuhume tuhumen da ake yi masa, kafin daga bisan ya amince da su, abinda ya sa lauyansa ya nemi a yi masa sassauci, saboda a cewar sa ya yi nadama don haka ne ma ya amince don gudun ɓata wa kotu lokaci.

Mai shari’ar Emeka Nwite ya kama Maitangaran da laifi, inda ya yanke masa hukuncin shekaru ashirin, ya kuma umurci shugaban hukumar kula da gidajen yari ta kasar ya ajiye Maitangaran a duk gidan yari da ya so, kuma a sanya shi a wani shiri na gyaran hali da kuma canza masa aƙida.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!