Labarai
Kotu ta kori ƙarar da Ɗan Zago ya kai Abdullahi Abbas
Babbar Kotun tarayya da ke Kano ƙarƙashin mai shari’a AM Liman ta kori ƙarar da Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya shigar gabanta na ƙalubalantar shugabancin Abdullahi Abbas.
Yayin zaman Kotun na yau mai shari’a ya ce, ya kori shari’ar ne saboda masu ƙara basu sanya hukumar zaɓe a cikin ƙorafinsu ba.
Lauyan waɗanda ake ƙara Barista Marcellunus Duru ya shaida wa Freedom Radio cewa, dama tun farko sun shaidawa Kotun cewa bata da hurumin sauraron ƙarar.
Shi ma lauyan masu ƙara Barista Rabi’u Sa’id Rijiyar Lemo ya ce, ƙorafinsu ba a kan INEC ba ne, suna ƙorafi ne kan rashin cika sharuɗan cancantar Abdullahi Abbas a matsayin shugaba.
Barista Rijiyar Lemo ya ce, Abdullahi Abbas bai sauka daga muƙaminsa ba har lokaci ya ƙure, saboda haka zasu nazarci hukuncin kotun domin ɗaukar mataki na gaba.
You must be logged in to post a comment Login