Labaran Kano
Kotu ta kori shari’ar matar da ake zargi da kisan ƴar aiki
Kotun majistiri mai lamba 8 da ke gyaɗi-gyaɗi ta kori ƙarar matar nan Fatima Hamza da ake zargi da kisan ƴar aikinta.
Lauyan Gwamnati Muhammad Sani ya shaida wa kotu cewa, sun yi shawara da ma’aikatar shari’a inda suka gano babu ƙwaƙƙwarar shaida kan tuhumar da ake wa Fatiman.
A don haka lauyan ya buƙaci kotu da ta kawo ƙarshen takardar tuhumar da aka gabatar.
Lauyan wadda ake zargi Barista Ibrahim Abdullahi Cheɗi bai yi suka ba.
Ƙarshe mai shari’a Ibrahim Khalil ya kori shari’ar nan take.
Sannan lauyan Gwamnati ya buƙaci a gayyato wasu ƴan jarida da wasu mutane biyu da ya ce, sun zuzuta labarin.
A baya da rundunar ƴan sandan Kano ta ce, ta samu shaidu uku da za su bayar da shaida a kanta a gaban kotu.
A lokacin, mai magana da yawun ƴan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, samun hujjojin ne ya sanya suka gurfanar da ita a gaban kotu.
You must be logged in to post a comment Login