Labarai
Kotu ta sake bayar da beli Godwin Emefiele
Babbar kotu da ke Ikeja a jihar Lagos da ke ta bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele
Alkalin kotun Mai shari’a Rahman Oshodi, ya bayar da shi belin ne a kan kuɗi har naira miliyan 50 tare da gabatar da masu tsaya masa mutum biyu kan irin yawan kuɗin.
Haka kuma, Kotun ta ce ya zama wajibi mutanen biyu su kasance ma’aikata sannan kuma suna da shaidar biyan haraji ta shekaru uku da suka biya gwamnatin jihar Lagos.
BBC ta ruwaito cewa, Alƙalin ya kara da cewa, ya gamsu da ƙa’idar cika belin ta naira miliyan ɗaya da tun farko aka bai wa Henry Isioma-Omoli wanda shi ma yake fuskantar shari’a kan wata tuhuma gaban alƙali Olufunke Sule-Hamzat na babbar kotun jihar da ke zamanta a Yaba.
You must be logged in to post a comment Login