Babbar kotu tarayya da ke birnin Ikko, ta sanya ranar 9 ga watannan da muke ciki a matsayin ranar da za ta yanke wa Idris Olanrewaju Okuneye da aka fi sani da Bobrisky hukunci bayan da ta same shi da laifin wulaƙanta naira.
Haka kuma alkalin kotun, ya bayar da umarnin ci gaba da tsare matashin wanda ya sauya halittarsa zuwa ta mata da a ci gaba da kula da shi a hukumar EFCC.
BBC, ta ruwaito cewa, kafin samun sa da laifi, Bobrisky ya shaida wa kotu cewa ba shi da masaniya kan dokar hana wulaƙanta naira.
Sai dai Alƙalin ya shaida masa cewa rashin sani ba hujja ba ne a doka.
Bobrisky ya kuma nemi alƙali da ya sake ba shi dama ta yin amfani da shafinsa na sada zumunta wajen ilmantar da mabiyansa game da illar yin liƙi da kuɗi.
Idan za a iya tunawa, a ranar Larabar da ta gabata ne hukumar EFCC ta kama Bobrisky kan zargin wulaƙanta kudin Nijeriya watau naira.
You must be logged in to post a comment Login